A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, wasu ma'aikata da gwamnatin Nasir El-Rufa'I ta sallama daga aiki na kukan cewa sun fada cikin mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin jihar ta sallame su daga aiki.
Ma'aikatan sun shaida wa BBC cewa abin da za su ciyar da iyalansu ma na fin ƙarfinsu.
Tun a shekara ta 2017 aka yi musu ritayar dole, inda suka yi zargin cewa ba a biya su haƙƙoƙinsu ba. Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta yi musu tayin koya musu sana'ar noma amma da dama sun yi biris da ita.
Kazalika, sun ce an katse musu rayuwa da su da iyalansu, kasancewar abin da suke taimaka wa wasu da shi ya fi ƙarfinsu, kasancewar ba su shirya wa sabuwar rayuwar da suka samu kansu a ciki ba.
"Ina nadamar shiga aikin koyarwa'
Cikin wadanda aka yi wa irin wannan sallamar har da malaman makaranta.
Malam Ahmed Mato Lere ya ce ya shiga halin tasku bayan an yi masa ritaya, har ta kai ga yana nadamar rungumar koyarwa a matsayin sana'a.
"Na shiga cikin wani yanayi. Nakan kwanta da matata ina tunanin abin da zan karya da safe," in ji shi.
Ya ƙara da cewa: "Ana bi na bashi na kuɗin makarantar yara. An nemi ma a kore su amma ina zuwa ina bayar da haƙuri ana ƙyale su.
"Na yi nadama tsakanina da Allah cewa da na san zan tsinci kaina a irin wannan lamari wallahi tallahi da ban yi sana'ar koyarwa ba."
Yadda ta kaya tsakanin NLC da El-Rufa'i a yajin aikin Kaduna
'Ina da shekara 48 aka yi mani ritayar dole'
Hajiya Hadiza Ahmed ma'aikaciyar ƙaramar hukuma ce da aka yi wa ritaya a matakin albashi na 13.
"An ce akwai tsari da gwamnati ta fito da shi cewa duk waÉ—anda aka sallama daga 2017 idan ya cika shekara 50 za a fara ba shi fansho, idan kuma ba ka cika 50 ba za a ba ka fansho ba.
"Idan kuma ka fara karɓar fansho ba za a ba ka giratuti ba [kuɗin sallamar ma'aikaci," a cewar Hadiza.
0 Comments