Header Ads Widget

Ya kamata APC ta tsayar da dan takarar shugaban ƙasa daga kudancin Najeriya'

 




Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan majalisar dattawan Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya kamata jam'iyyarsa ta APC mai mulkin Najeriya ta danƙa wa kudancin ƙasar takarar shugaban kasa.

A wata hira ta musamman da ya yi da Ibrahim Isa na BBC Hausa, Sanata Shekarau ya ce ana buƙatar yin hakan ne don tabbatar da adalci.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:

Tambaya: Ana ganin jam'iyyarku ta ƙi taɓo batun tsarin karɓa-karɓa, kuma ana ganin a nan ne za a iya kai ruwa rana. Ta yaya kake ganin APC za ta iya kauce wa wannan?

Amsa: A cikin tsarin mulkin APC ba a rubuta zancen karɓa-karɓa ba, amma ni na yarda akwai tsarin mulki na hankali.

Yanzu kamar tsarin shiyya-shiyya da ake yi ai ba ya cikin kundin tsarin mulki na Najeriya, amma tsari ne mai kyau, yanzu babu abin da za ka yi ba ka shigo da wannan ciki ba.

To haka ma zancen shugabanci tsakanin kudu da arewa, idan aka yi watsi da wannan to gaskiya ba a yi wa juna adalci ba, kuma ba mu yi wa tarihin kafuwar Najeriya adalci ba.

Ni ina da ra'ayin cewar wajibi ne don kowa ya ji cewar ana yi da shi.

Tambaya: Idan na fahince ka tun da yanzu Shugaba Buhari zai kammala wa'adinsa na biyu kana tunanin mulki ya koma kudu kenan?

Amsa: Sosai ma. Ni ina ganin ya kamata mu yi haƙuri mu jawo ƴan uwanmu na kudu mu da muke daga arewa. Ka ga ai da aka yi zaɓe, arewa ita kaɗai ba za ta yi ƙuri'ar samar da shugaban kasa ba, kudu ita kaɗai ma ba za ta yi ba, sai mun hadu kuma zaman tare muke.

Ni abin da na yarda da shi shi ne ba ma wai shiyya-shiyya ba, babu wata jiha a Najeriya yau da ba ta da wadanda za su iya yin shugabanci a kasar nan.

Rashin yin wannan shi zai daɗa kawo rarrabuwar kawuna, wasu su dinga jin ba a yi da su ko ba a so a ba su dama ko wasu sun fi iyawa, wannan duk bai kamata ya taso ba.

Ita harkar siyasa al'amari ne na yawa, kuma arewa ana tunƙahon tana da yawan masu kaɗa ƙuri'a.

Tambaya: Ba kwa ganin za ku iya rashin dabara idan abokan hamayyarku kuma suka fitar da ɗan takara daga arewa?

Amsa: To ai kullum kana yi ne kana kallon me ye adalci. Dukkanin jam'iyyun da PDP da APCn a yanzu suna cikin wannan hasashe na kowa na kallon me wane zai yi da watakila zai sha gabana.

Amma ni abin da nake son kowaccensu ta kalla, kar mu tsaya kallon me wane zai yi ya sha gaban. A'a mu kalli me zan yi ya zama adalci, idan ka yi adalci, adalcinka da nagartar wanda ka fitar su za su yi jagora.

Tambaya: Me kake gani kan sauya sheƙar da wasu ke yi zuwa jam'iyyar APC?

Amsa: Jam'iyyar APC ana ƙara samun nasara tun da ga shi a ɗan tsakanin nan cikin wata biyu da suka wuce har an samu gwamnatocin jihohi biyu sun ƙaru a cikin jam'iyyar.

Wannan ba ƙaramar nasara ba ce, kuma ana ta samun ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi ana ta karɓarsu a jam'iyyar.

Illa dai kawai a kullum ita harkar siyasa mutane suna son su dinga jin motsi. An kusa shekara ana so a yi babban taro wato convention, to jam'iyyar ta yunƙura ta fitro da tsarin sabunta katin yan jam'iyya kuma hakan ya kawo nishadi.

Abin da ya rage shi ma kuma ga shi an fitar da tsari a kan tebur za a yi congress. Za a yi zaɓen tun daga mazaɓa zuwa ƙaramar hukuma zuwa jiha zuwa shiyya.

Abin da ba a fitar ba a yanzu kuma na tabbatar suna nan suna aiki a kai shi ne yadda za a raba muƙamai na ƙasa.

Post a Comment

0 Comments