Header Ads Widget

Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan


 

Sarki Nuhu Bamalli

ASALIN HOTON,MASARAUTAR ZAZZAU

Wannan rahoto ya yi duba game da wasu abubuwa da suka faru a Najeriya a makon da muke bankwana da shi, inda muka zaƙulo muhimmai daga cikinsu.

Al'ummar wasu yankunan Zaria na cikin fargaba da É—imauta

Al'ummar wasu yankunan Zaria cikin jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun shiga fargaba da ɗimauta tun bayan harin da 'yan fashin dajin suka kai a ƙarshen mako.

Harin ya yi sanadin sace aƙalla mutum takwas.

Shaidu sun ce maharan É—auke da bindigogi ne suka shiga sabuwar unguwar Kofar Gayan inda suka kutsa cikin gidaje suka yi awon gaba da iyalai ciki har da 'yan mata da samari.

Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da 'yan bindiga suka sace É—alibai da malamai a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke garin na Zaria.

An 'kashe 'yan fashi 80' bayan sun sace dalibai da dama a jihar Kebbi

Bindiga

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanai daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu jami'an tsaron ƙasar sun kashe 'yan bindiga kusan 80 a yunƙurinsu na kuɓutar da yara 'yan makaranta da miyagun suka sace.

A ranar Alhamis da rana ne 'Æ´an bindigar suka kutsa makarantar FGC Yauri tare da sace yaran.

Kazalika, sojoji sun kuɓutar da wasu daga cikin yaran.

Wasu shaidu sun shaida wa BBC cewa sun ga gawar ɓarayin dajin fiye da 80.

Suka ƙara da cewa an yi gumurzu sosai tsakanin dakarun tsaro da ɓarayin dajin a Ƙaramar Hukumar Sakaba ta jihar Kebbin.

Ganau sun ce 'yan bindigar sun tafi da dalibai da yawa sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya gaya wa BBC cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar kana suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba daliban sannan suka tafi da su.

Wasu mutane sun ce an kai dalibai da dama asibiti domin yi musu maganin harbin bindiga sakamakon raunukan da suka samu yayin da suke tserewa daga harin na 'yan bindiga.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Wakilan Najeriya, Muhammad Bello Ingaski, ya shaida wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun sace dalibai maza da mata.

Shugaba Buhari a Borno

Muhammadu Buhari

ASALIN HOTON,STATE HOUSE

A ranar Alhamis ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Shugaban na Najeriya ya isa filin jirgin saman Maiduguri da safiyar ranar ta Alhamis kuma daga nan ya shiga aiwatar da abubuwan da suka kai shi jihar.

Wata sanarwa da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaÉ—a labarai Isa Gusau ta ce Shugaba Buhari ya bayyana cewa 'na yi matukar jin dadi' bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin ayyuka 556 da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Shugaba Buhari ya yi tsokaci na musamman kan Makarantar Koyon Ayyukan Hannu da ya kaddamar a Muna, wadda ya bayyana a matsayin wata cibiya da za ta samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando ga matasa ta yadda zai yi wahala kungiyar Boko Haram ta dauke su, a cewar Isa Gusau.

An tsara makarantar ce domin mutum 1,500 su samu horon sana'o'i a duk shekara, in ji gwamnatin ta jihar Borno.

Da gaske jiragen sojin Najeriya sun halaka shanu 1,000 a Nasarawa?

Shanu

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin sojin Najeriya ya halaka shanu sama da 1,000 a wasu jerin hare-hare kan matsugunan Fulani makiyaya a yankunan ƙananan hukumomin Keana da Doma na jihar Nasarawa a yankin tsakiyar Najeriya.

Sai dai Daraktan hulÉ—a da jama'a na rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya shaida wa BBC cewa batun ba haka yake ba, babu ko saniya É—aya da aka kashe a lokacin aikin sojin.

Amma shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa Muhammad Kiruwa Ardon Zuru, ya gaya wa BBC cewa jirgin sojojin saman Najeriyar ya ƙaddamar da hare-haren ne a tsakanin ranakun Alhamis 10 ga watan Yuni da Lahadi 13 ga watan Yuni.

"Mun samu labarin kashe shanun daga jama'armu da ke waɗannan yankunan a lokacin da jiragen yaƙin sojin suka shafe kwanaki huɗu suna kai hare-hare a yankin,'' in ji shi.

Ardon Zurun ya kara da cewa ba a samu asarar rayukan mutane ba amma kuma hare-haren sun hallaka tare da jikkata wasu shanun a yankunan.

"Yanzu haka muna jiran cikakkun rahotanni daga shugabannin yankunan da za mu tantance mu tura wa shugaban kwamitin amintattu wato Sarkin Musulmi cewa ga abin da ke faruwa, domin a tura wa shugabannin sojojin," in ji shi.

Najeriya za ta buga wa Gambia kuÉ—i

Buhari da shugaban Gambia

ASALIN HOTON,NG PRESIDENCY

Babban Bankin Najeriya CBN ya amince ya buga wa ƙasar Gambia nau'in kuɗinta na Dalasi.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin takwaransa na Gambia Buah Saidi yayin da ya ziyarce shi da tawagarsa a ranar Talata.

Mista Emefiele ya ce Najeriya na da damar da za ta iya bugawa Gambia kudin, da yake ta jima tana buga kudi tun shekarun 1960.

Tun da farko gwamnan babban bankin Gambian ya ce kasarsa na fama da karancin kuɗi, sannan suna fatan samun ƙwarewa wajen buga kuɗin daga Najeriya.

Ana barazanar halaka ni - Shugaban EFCC AbdulRasheed Bawa

AbdulRasheed Bawa

ASALIN HOTON,EFCC

Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya ta'annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce ana ta aika masa da sakonnin barazana ga rayuwarsa tun bayan da ya hau shugabancin hukumar.

Ya bayyana hakan ne yayin wani shirin barka da safiya na gidan talabin É—in Channels dake Najeriya.

''A makon da ya wuce ina New York aka kira wani babban mutum a kasar nan aka gaya masa cewa za mu halaka wannan yaron da yake shugabancin hukumar EFCC'', in ji Bawa.

Ya ƙara da cewa ''Toh ka ga wannan yana nuna maka irin yadda cin hanci ke yaƙarka a lokacin da kai kake yaƙi da shi, gaskiya ne duk inda ka waiwaya za ka ga cewa akwai matsalar nan, amma ina da kwarin guiwar cewa za mu karo karshenta a Najeriya", a cewarsa.

Post a Comment

0 Comments