Mahukuntan Kwalejin Tarayya ta Birnin Yawuri cikin jihar Kebbi a Najeriya sun ce har zuwa daren jiya suna ci gaba da aikin tattara alƙaluman ɗaliban da 'yan fashin daji suka sace.
Tuni dai aka rufe makarantar, wadda ta tabbatar da cewa malamai da sauran ma'aikatanta bakwai ne ke cikin ɗaliban da aka sace.
Har zuwa wayewar garin Juma'a ana ƙoƙarin mayar da ɗaliban da suka rage hannun iyayensu, ciki har da waɗanda suka fito daga wajen jihar Kebbi.
Da tsakar ranar Alhamis ne maharan suka auka wa makarantar inda suka ci ƙarfin jami'an tsaron da ke wurin kafin su yi awon gaba da ɗalibai da dama.
Wani jami'i a makarantar da ya nemi ba sai an ambaci sunansa ba, ya ce da wuya su iya sanin adadin ɗaliban da aka sace cikin sauri, saboda iyaye da dama sun je sun tafi da 'ya'yansu gida.
Ya ce: "Iyaye dai da yawa na ta zuwa neman ƴaƴansu, kuma an buɗe rijista an ce duk wanda bai ga yaronsa ba to ya rubuta don a samu taƙamaimai yawan waɗanda aka sace.
"Amma dai an tabbatar mutum bakwai ne suka ji rauni. Sannan ga ɗaliban sauran garuruwa kuma mun samo motocin da za su kai garuruwansu. A ƙalla mutum 10 ne za a kai.
Sai dai ya ce har yanzu babu taƙamaimai yawan ɗaliban da aka sace. "Kowa dai ra'ayinsa yake faɗa. Da abin ya faru mun so ɗalibai su tsaya mu ƙirga yawansu amma iyaye suka ta da hankali suka ƙi suka kwashe su.
"Don haka ba mu da bayanin taƙaimaimai yawansu sai dai nan da ɗan lokaci kaɗan za mu duba rijistar mu gane yawan waɗanda aka kwashe
Naomi Yakubu, wata uwa ce ga ɗaya daga cikin ɗaliban Kwalejin wadda aka harbi yaronta a wannan hari, ta kuma yi wa BBC Hausa bayanin halin da ake ciki.
"Ina nan sai aka zo aka ce min to ga fa abin da ya faru. Ko da muka kama hanyar makarantar sai aka ce ga fa wani yaro da aka harba. Tun a lokacin zuciyata ta raya min cewa ɗana ne.
"Ina kuwa zuwa na samu shi aka harba har harsashi biyu. GAskiya yanayin dai da na tarar da shi sai godiyar Allah.
"Yanzu dai ga shi nan a kwance. Na ɗan yi magana da shi, inda ya ce min da suka fito sai suka ga ana ƙoƙarin kwashe ƙananan yara. Sai ya riƙe su suna gudu shi ne fa sai harbin ya same shi a baya.
"To bayan an harbe shi kuma sai ɓarayin suka ɗauke shi har sun sa shi a mota sai suka ga jini na zuba sai suka fitar da shi daga motar.
Misis Naomi ta ce a yanzu sai dai a ce jin ɗan nata da sauƙi likitoci na kula da shi.
"Ikon Allah ne ya ceto da yaron nan ba na mutum ba don jinin da ya zuba daga jikinsa. Don da ƙyar wani malamai ya yi maza ya ɗauke shi aka garzaya da shi asibiti."
0 Comments